Aller au contenu principal

Sadiya Umar Farouq


Sadiya Umar Farouq


Sadiya Umar Farouk (an haife ta a ranar 5 ga watan Nuwamba shekara ta alif dari tara da sabain da hudu 1974), ’yar siyasa ce a Nijeriya kuma ita ce ministar harkokin agaji, kula da bala’i da ci gaban al’umma a Najeriya.

Siyasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta minista a watan Yulin shekarar 2019, Farouk a shekaru ta zama mai mafi i karancin shekaru a cikin ministocin gwamnatin tarayya. Dangantakar ta da Shugaba Buhari ta samo asali ne tun zamanin Buhari a matsayin jagora kuma dan takarar shugaban kasa na rusasshiyar Congress for Progressive Change lokacin da Farouk ya kasance ma'ajin jam'iyyar CPC na kasa sannan daga baya ya kasance ma'ajin jam'iyyar All Progressives Congress.

A watan Disamba na shekara ta 2019, ofishin shugaban kasa ta tuhumi Sadiya don yin amfani da karfin da ya wuce ikon matsayinta na aiki ta hanyar daukar karin mataimaka fiye da yadda hukuma ta kuma amince da shi da kuma jinkirta kudaden wata-wata na masu sa kai na N-Power, shirin tsoma bakin jama’a na gwamnatin tarayya. Bikin auren Sadiya-Sadique: Shugaban Sojan Sama, Ministan Jin kai Aure ya daɗe yana zuwa - majiyoyin dangi

Duk da kalubalen kasafin kudin Najeriya tare da karancin kudaden shiga, Ministan, yayin da yake fuskantar dumbin munanan manufofin yakin neman zabe, da karfin hali aiwatar da ayyukan Covid-19 da Shirye-shiryen saka hannun jari na gwamnatin tarayya.

Ilimi

  • FGGC, Gusau [1]
  • Jami'ar Ahmadu Bello, dake Zariya

Kara Karantawa

Karanta nan: https://prnigeria.com/2020/09/24/sadiya-sadique-wedding

Manazarta

Collection James Bond 007


Text submitted to CC-BY-SA license. Source: Sadiya Umar Farouq by Wikipedia (Historical)