Aller au contenu principal

Kano (birni)


Kano (birni)


Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba'in da huɗu. Kano gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin ƙasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda mazauna cikin sa ke magana da harshen Hausa. Kano ita ce gari mafi yawan jama'a a Najeriya gaba ɗaya.Yaren daya Sahara a duniya gaba daya. Cikin birnin Kano akwai ƙofofi kamar haka Kofar Gadon Kaya, Kofar Famfo, Kofar Na'isa, Kofar nasarawa, Sabuwar Kofa, Kofar Mazugal, Kofar Dawanau, Kofar Dan Agundi, Kofar Dukawuya, Kofar Ruwa, Kofar Kansakali, Kofar Mata.

Yawan mutanen da suke garin Kano ya haura kimanin mutane miliyan goma (10,000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida (2006). Jihar Kano tana da matukar tasiri a yawan mutane a Najeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan mutane a Najeriya. Idan ka zo Kano za ka samu mutane daga ko'ina a fadin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, haka kuma za ka tarar da mutanen Sin (wato China), da kuma na kasashen Larabawa har da turawan yammacin duniya. Mutanen kano sun shahara wajen ilimin addini sosai.

Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunƙasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma, tarihin Kano ya nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.

Tarihin Kano

Anan za'a sa takaitaccen tarihin Kano

Mutanen Farko

Kano Jalla babbar Hausa ta dabo tumbin giwa ko da me ka zo amfika wannan shi ne kirarin da akewa wanna katafaren gari. Idan ana zancen su wane suka fara zama a Kano to tarihi zai iya cewa kamar yanda Allah subhanahu wata'ala ya yi mutane a sauran sassan Duniya hakama ya ajiye bayin sa a garin Kano.

sai dai kabilu da dama sun zo kasar Kano kamar su Madatai da Dala. zuwan wadannan kabilu ya kara habaka garin Kano kabilar Madatai ta riga Kabilar Dala zuwa Kano da suka zo wannan gari mai Albarka sun sami wasu kabilu masu yawa a Kano Amma ana ce da su Kabilun Kwararrafa.

Kano a matsayin Jiha

Tarihin Kano tun da ta zama Jiha a Kasar Najeria, cigaban da ta samu, da kuma matsalolin da take fuskanta

Yanayi

Sanannun Mutane

Sannanun Mutane a Kano sun hada da:

  • Nasiru Yusuf Gawuna
  • Abdullahi Umar Ganduje; Tsohon gomnan jihar
  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hisbah
  • Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo, Malamin addinin musulunci
  • Alhaji Aminu Dantata. Attajiri kuma dan kasuwa.
  • Alhaji Aliko Dangote. Shahararren mai kudi, Attajiri kuma dan kasuwa.
  • Alhaji Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin Kano), Dan siyasa ne kuma yana daga cikin manyan mutane a Jihar Kano.
  • Ado Bayero. Sarki na goma sha uku (13) a jihar Kano.
  • Sanusi Lamido Sanusi. Shohon gwamnan Central Bank of Nigeria (CBN), kuma sarki na Goma sha huɗu a jihar Kano.
  • Abdulsamad Rabiu. Shugaban kanfanonin BUA, dan kasuwane kuma attajiri.

Manazarta


Text submitted to CC-BY-SA license. Source: Kano (birni) by Wikipedia (Historical)


PEUGEOT 205