Aller au contenu principal

Harin bam a Konduga, 2018


Harin bam a Konduga, 2018


A ranar Juma'a 16 ga watan Fabrairu 2018, an kai harin ƙuna baƙin wake sau uku a Konduga, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Lamarin

Wasu ‘yan ƙuna baƙin wake biyu sun tayar da bama-baman da ke jikinsu a wata kasuwar kifi mai cike da cunkoson jama’a da misalin karfe 8:30 na dare. Mintuna huɗu bayan haka, bam na uku ya tashi a kusa da wurin.

Hare-haren sun kashe tsakanin mutane 17 zuwa 22 tare da jikkata tsakanin 22 zuwa 70. Ɗaya daga cikin maharan mace ce, yayin da sauran biyun kuma maza ne. An kai waɗanda suka jikkata a harin zuwa asibiti a birnin Maiduguri.

Bayan harin

Ba a samu labarin lamarin ba, har sai washegari. Babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, amma mayakan Boko Haram sun sha kai manyan hare-hare a Konduga a baya (ciki har da kisan kiyashi a watan Janairu da Fabrairun 2014 ) da kuma (ciki har da harin kunar bakin wake sau uku a watan Yunin 2019 ).

Manazarta


Text submitted to CC-BY-SA license. Source: Harin bam a Konduga, 2018 by Wikipedia (Historical)

Articles connexes


  1. Harin bom a Konduga, 2019