Aller au contenu principal

Prime 9ja Online


Prime 9ja Online


Prime 9ja Online Jarida ce ta yanar gizo ta Najeriya wacce Prime 9ja Online Media ke bugawa a jihar Edo, Najeriya mai bayar da labarai da nazari akan siyasa, kasuwanci, nishadantarwa, wasanni, da sauransu. Chima Joseph Ugo ce ta ƙaddamar da gidan yanar gizon a shekarar 2016 da nufin wadata 'yan Najeriya da 'yan Afirka sahihan labarai da bayanai masu inganci.

Tarihi

Prime 9ja Online gidan yanar gizo ne na yaɗa labarai da Chima Joseph Ugo ta kafa a shekarar 2016 mai hedikwata a Okada, Edo, Najeriya.

A cikin watan Yuni 2022, Stamp Nigeria ta sanya Prime 9ja Online a cikin manyan jaridu 19 da ke haɓɓaka cikin sauri a Najeriya.

A watan Maris 2023, jaridar sun ƙaddamar da sashin labarai a cikin turanci Pidgin.

Pidgin

Baya ga wallafa labarai cikin harshen turanci, Prime 9ja Online kwanan nan sun ƙaddamar da fara wallafa labarai da Pidgin na gidan yanar gizon su, Prime 9ja Online Pidgin. Manufar ita ce ’yan Najeriya waɗanda za su iya fahimtar Turancin Pidgin fiye da Turanci na asali, su samu labarai cikin sauƙi. Wannan yunƙurin yana tabbatar da cewa suna kawo labarai zuwa ga asalin yan yankin, da ƙarin bawa mutane damar samun ingantattun labarai da bayanai masu inganci.

Manazarta

Hanyoyin haɗi na Waje

  • Official website in English language
  • Official website in Nigerian pidgin

Collection James Bond 007


Text submitted to CC-BY-SA license. Source: Prime 9ja Online by Wikipedia (Historical)


INVESTIGATION