Aller au contenu principal

Salvador Dalí


Salvador Dalí


alvador Domingo Felipe Jacinto Dalí i Domènech, Marquess din Dalí na Púbol (11 May 1904 – 23 Junairun 1989), wanda akafi sanii da Salvador Dalí, Mai zane ne dan kasar Sipnaiya wanda yayi fice da baiwarsa na zane, kwarewa a zana mutane, da zanukansa na musamman masu ban al'ajabi.

An haife shi a Figueres, Katalunya, Hispania a shekara ta 1904, ya mutu a Figueras a shekara ta 1989. Dani ya samu iliminsa na zane a Madrid. A dalilin horn da ya samu daga malaman Impressionist da Renaissance tun yana karami, ya zamo mabiyin tafarkin zane na cubism da kuma avant-garde.

Ya samu kusanci da kungiyar Surrealism a shekarun 1920s sannan ya koma kungiyar a shekarar 1929, nan da nan ya zamo daya daga cikin muhimman jagororin kungiyar. Aikinsa da yafi kowanne shahara The Persistence of Memory, ya kammala shi ne a watan Agustan 1931. Kuma yana daya daga cikin ayyukan Surrealist mafi shahara. Dali ya kwashe daukakin rayuwarsa a lokacin Yakin Basasar Hispaniya (1936 to 1939), kafin ya koma Amurka a 1940, inda ya samu nasarori da dama na kasuwanci. Ya dawo kasar Sipaniya a shekarar 1948 inda ya sanar da dawowarsa zuwa addinin Katolika inda ya fara habaka salonsa na “nuclear mysticism".

Tarihin Rayuwa

Kuruciya

An haifi Salvador Dali a ranar 11 ga watan Mayun 1904, da misalin karfe 8:45 na safe, a hawa na farko na ginin Carrer Monturiol a birnin Figueres, na yankin Empordà, kusa da iyakar Faransa dake Kataloniya, kasar Sipaniya. Babban wan Dali mai suna Salvador (wanda aka haifa a ranar 12 ga watan Oktoban 1901) ya rasu a sanadiyyar cutar gastroenteritis watanni tara kafin haihuwar Dali, a ranar 1 ga watan Augustan 1903. Mahaifinsa, Salvador Luca Rafael Aniceto Dalí Cusí (1872–1950), lauya ne kuma magatakarda mai matsakaicin karfi, tsatsauran mabiyin addinin gargajiya dan Katalan, wanda matarsa, Felipa Domènech Ferrés (1874–1921) ta saba duk wani ka'idojinsa, inda ta karfafawa danta gwiwa da ya cigaba da bibiyar sana'ar zane. A lokacin rani na shekara ta 1912, iyalin sun koma bene na sama acikin ginin Carrer Monturiol 24 (hawa na 10 a yanzu)

Manazarta


Text submitted to CC-BY-SA license. Source: Salvador Dalí by Wikipedia (Historical)



INVESTIGATION